Bayanan ‘yansandan China ya bankado mummunan yanayin da musulmai ke ciki a tsare

43

Dubban hotuna daga wajen daure mutane na sirri a birnin Xinjiang na kasar China, tare da dokar harbe duk wadanda suka yi kokarin tserewa, na daga cikin dimbin bayanan da aka samu ta hanyar kutse cikin kwamfutocin ‘yan sanda a yankin.

Takardun bayanan ‘yan sandan Xinjiang, kamar yadda ake kiransu, an mika su ga BBC a farkon wannan shekarar.

Wallafa bayanan na zuwa ne daidai lokacin da kwamishiniyar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Michelle Bachelet ta isa kasar China a kwanakin baya, domin ziyarar da ta kai birnin Xinjiang da ta jawo cece-ku-ce.

Bayanai sun nuna yadda China ke amfani da abin da gwamnatin kasar ta kira sansanonin sake ilimintarwa da gidajen yari a matsayin guraren tsare Musulman kasar ‘yan kabilar Uygur.

Ikirarin da gwamnati ta yi na cewa sansanonin sake ilimintarwa da aka gina a birnin Xinjiang tun daga shekarar 2017 ba komai ba ne illa makarantu, ya ci karo da umarnin ‘yan sanda na cikin gida, da ka’idojin tsarewa da kuma hotunan da aka wallafa na wadanda aka tsare, da ba a taba ganin irinsu a baya ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 − 3 =