Badaru ya umarci masu rike da mukaman siyasa dake takara su yi murabus

59
Gwamnan Jihar Jigawa Muhammadu Badaru

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati da ke da sha’awar tsayawa takara da su yi murabus daga yau Laraba 11 ga Mayu zuwa Litinin 16 ga Mayu 2022.

A cewar wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Habibu Nuhu Kila ya fitar, kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar Alhaji Bala Ibrahim Mamsa ne ya bayyana wannan umarni na gwamnan a yau bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar wanda Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya jagoranta a gidan gwamnati dake Dutse.

A cewar sanarwar, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yana yi wa duk masu neman mukamai fatan alheri a kan burinsu na siyasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 2 =