Ana zaman dar-dar a Birnin Kudus gabannin tattakin da matasan Isra’ila za su gudanar

56

Dubban Yahudawan Isra’ila ne za su gudanar da wani tattaki a yankunan musulmi a tsohon birnin Kudus duk da Falasdinawa sun yi gargadin cewa hakan zai iya haifar da tashin hankali.

Bikin na shekara-shekara na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula bayan watanni da aka shafe ana munanan hare-hare.

Ana gudanar da tattakin ne a bikin Ranar Kudus ta Isra’ila, domin murnar karbe gabashin birnin Kudus a yakin shekarar 1967.

Isra’ila dai na kallon birnin Kudus a matsayin babban birninta, lamarin da galibin kasashe da Falasdinawa suka yi watsi da shi.

Matsayin birnin ya shiga tsakiyar rikicin Isra’ila da Falasdinu. Falasdinawa dai na ikirarin mamaye yankin Gabashin Kudus da Isra’ila ta yi a matsayin babban birninsu, ko da yake Isra’ilan ta ce ba za a sake raba birnin ba.

A shekarar da ta gabata wani kazamin rikici na kwanaki 11 tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a Gaza ya barke a bikin Ranar Kudus lokacin da mahukuntan Hamas na Gaza suka harba rokoki zuwa birnin bayan da ‘yan sandan Isra’ila da Falasdinawa suka fafata a wani wuri mai tsarki a tsohon birnin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 7 =