An sace matafiya bayan hatsri ya jawo asarar rayuka a hanyar Kaduna-Abuja

65

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun sace matafiya da dama a hanyar Abuja zuwa Kaduna a jiya.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a garin Katari da misalin karfe 4 da rabi na yamma.

A cewar majiyar, an ga motoci da yawa da babu kowa a ko wane bangare na hanyar, lamarin da ke nuni da cewa an sace mutanen ne ko kuma sun gudu cikin daji.

A wani batun kuma, wani hatsarin mota da ya afku a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, ya yi sanadiyyar mutuwar fasinjoji 20.

Wani ganau wanda ya ce hatsarin ya rutsa da motar safa da tirela ya yi sanadiyar mutuwar mutane 17 da suka hada da mata biyu da yaro daya, yayin da wasu biyu suka tsira.

Majiyar ta kuma ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5 na safiyar jiya lokacin da motar bas din ta kutsa cikin wata tirelar siminti da aka ajiye akan titin.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa Hafiz Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − 6 =