Rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba ta tabbatar da cewa wani jami’in soji Laftanar Kanal Eminike ya bata yayin da sojoji shida da wani jami’in dan sanda suka mutu a wani rikici da ya barke tsakanin ‘yan kabilar Kutep da Fulani makiyaya a yankin Tarti da ke karamar hukumar Takum a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Usman Abdullahi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a Jalingo, babban birnin jihar.
Ya ce Kanal Eminike shi ne kwamandan da ke jagorantar ayyukan yaki a yankin da rikicin ya shafa.
Kisan ya zo ne wata guda bayan an kashe ‘yan sanda uku a Takum a wani rikici tsakanin ‘yan kabilar Kutep da ‘yan kabilar Jukun a lokacin bikin al’adun kabilar Kutep na shekara-shekara.
Usman Abdullahi ya yi zargin cewa ‘yan kabilar Kutep da Fulani ne ke da alhakin kashe sojojin da dan sandan.
Ya ce an tura karin sojoji da ‘yan sanda yankin domin samar da zaman lafiya yayin da ake ci gaba da neman jami’in sojan da ya bata.