Engr. Muaz Magaji Ɗansarauniya, tsohon kwamishinan aiyuka da raya ƙasa a Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kuma tsohon shugaban kwamitin duba aikin janyo bututun iskar Gas a Kano, ya sayi fom ɗin takara a jam’iyyar PDP.
Ɗansarauniya tin bayan wasu rikice-rikicen gida da suka cika jam’iyyar APC a jihar Kano ya baiyana fitar sa daga APCn tsagin G7 da Sanata Ibrahim Shekarau yake jagoranta, inda ya koma PDP.
Injiniya Muaz ya wallafa hotunansa a shalkwatar jam’iyyar PDP inda ya siyi fom ɗin sa na takarar gwamna.
Muazu Magaji dai a shekarar zaɓe ma dai ta 2019 ya baiyana aniyarsa ta takarar Gwamna tin yana tare da tsohon ubangidansa a jam’iyar PDP, Rabi’u Kwankwaso.