Shugaban Ukraine ya sake mika bukatar jawabi ga shugabannin Afirka

64

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sake gabatar da sabuwar bukatar yin jawabi ga shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka, a cewar shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, Moussa Faki ya ce ya samu wannan bukatar ne a wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Ukraine.

Mutane biyun sun kuma yi magana game da muradin Shugaba Zelensky na bunkasa alaka ta kud da kud da kungiyar Tarayyar Afirka.

Moussa Faki bai bayyana ko za a amince da bukatar ba amma ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa shugaba Zelensky ya dage kan bukatar warware rikicin da kasar Rasha ta hanyar lumana.

A farkon watan nan ne shugaba Zelensky ya yi wata ganawa da takwaransa na Senegal Macky Sall, shugaban kungiyar Tarayyar Afirka na yanzu, inda ya bukaci ya yi jawabi ga shugabannin Afirka.

Kasashen Afirka ne suka mamaye jerin kasashen da suka kauracewa kada kuri’a kan kudirin Majalisar Dinkin Duniya na dakatar da Rasha daga kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + 6 =