Najeriya ta fara fitar takin zamani zuwa Amurka

47

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya danganta karuwar karfin Najeriya na zama jigo a samar da takin zamani a Afirca da yadda gwamnati mai ci ta fara amfani da kudirorin da suka kamata.

Shugaban Kasar ya sanar da haka a yau lokacin da yake karbar bakuncin shugabannin kungiyar masu samar da takin zamani a Najeriya, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban kasar yace wannan gagarumin cigaban da aka samu cikin kankanin lokaci ya tabbatar da karuwar kwararowar masu zuba jari zuwa bangaren daga kamfanoni masu zaman kansu, lamarin da ya kawo arziki ga miliyoyin ‘yan Najeriya tare da riba mai yawa ga masu zuba jarin.

Ya bayyana jin dadinsa kasancewar yanzu an wuce lokacin karancin takin zamani a kasarnan, inda ya yabawa kungiyar bisa hada kai da gwamnati a aikin samar da takin zamani domin cigaban noma.

Shugaban kasar yayi amfani da lokacin wajen tilawar matakan da gwamnatinsa ta dauka da nufin magance dogaro da kasashen waje domin samun takin zamanin da wadatar abinci a kasarnan.

A wani batun kuma, Najeriya ta fara fitar da takin zamani na Urea zuwa kasashen Amurka, Indiya, Brazil, Mexico da Argentina.

Babban Daraktan Tsare-Tsaren kamfanin Dangote, Devakumar Edwin ne, ya bayyana hakan a lokacin da ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya jagoranci tawagar ‘yan jarida a rangadin aiki zuwa kamfanin takin Dangote a Ibeju-Lekki a jihar Legas.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, ministan tare da tawagarsa sun kuma zagaya matatar man fetur ta Dangote da ke Ibeju Lekki a Lagos.

Kamfanin Dillancin Labaran ya bayar da rahoton cewa, a ranar 22 ga watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfanin takin zamani na Dangote wanda shi ne katafaren kamfanin takin Urea mafi girma a nahiyar Afirka domin samar da ton miliyan uku a duk shekara a kashi na farko.

Da yake jawabi a wani sabon jirgin da aka kera don fitar da takin, Devakumar Edwin ya ce takin urea na Dangote da aka yi daga iskar gas taki ne mai inganci, don haka ana bukatarsa ​​a kasuwannin duniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − 1 =