Shahararren mamallakin otal-otal da masana’antu, Tahir Fadlallah, ya rasu yana da shekaru 78 a birnin Beirut na kasar Lebanon a safiyar yau.
An rawaito cewa an kwantar da mai Tahir Guest Palace a wani asibiti a Beirut a ranar 15 ga Afrilu kuma ya ci gaba da zama a asibitin har zuwa rasuwarsa.
An garzaya da Tahir Fadlallah daga Kano zuwa Beirut a ranar 23 ga Afrilu, 2020 bayan ya kamu da cutar corona.
Majiyoyi daga iyalansa sun shaida wa manema labarai cewa yana kwance a asibitin tun lokacin da aka kai shi birnin Beirut shekaru biyu da suka wuce.
Marigayin wanda ya bar mata daya da ‘ya’ya biyar, ya bar wasiyyarsa cewa duk inda ya rasu a binne gawarsa a Kano.
An haife shi a ranar 5 ga Fabrairu, 1948 a birnin Beirut na kasar Lebanon, Marigayi Tahir Fadlallah ya tare a Kano tare da iyayensa yana da shekaru biyu da haihuwa.