Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta kara yawan rumfunan zabe a jihar Kano daga 8,074 zuwa 11,222 domin saukakawa masu zabe.
Kwamishinan zabe na jihar Riskua Shehu ya bayyana haka a jiya yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron bita na yini daya kan rahotannin harkokin zabe a Kano.
Ya ce ya zuwa ranar 14 ga watan Janairu, mutane 77,255 daga cikin 128,628 ne kawai suka kammala rajistar zabe ta internet a Kano.
Ya ce rashin kammala rajistar ya samo asali ne saboda masu kada kuri’a sun jahilci yadda ake yin rajistar.
Ya kara da cewa hukumar ta gano sama da mutane 200,000 da aka yiwa rajista sau biyu a Kano a lokacin aikin rijistar da ya gabata.
Riskua Shehu ya ce ya kamata mutane su rika hakuri da abokan hamayyar su a siyasa.