Hisbah ta kai sumame shagunan sayar da giya a Jigawa

68

Rundunar Hisba ta jihar Jigawa ta kai samame gidan sayar da barasa na Takur Adua Dutse inda ta kama kwalaben giya dubu 1 da 249 da kwalaben giya mararsa ruwa katan 143.

Haka kuma rundunar Hisban ta kama mai sayar da giyar.

Kwamandan Hisba na jihar Jigawa Mallam Dahiru Garki ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Dutse, inda yace sun kai samaman tare da hadin gwiwar baturen yansanda na karamar Hukumar Dutse.

Ya kuma yabawa alumma bisa irin hadin kai da goyan bayan da suke baiwa yan hisba wajen gudanar da ayyukansu.

Hakazalika, rundunar Hisba ta jiha ta kai samame gidajen sayar da barasa guda uku a cikin garin Gumel.

Rundunar Hisba ta samu nasarar kama maza 11 da mace 1 mai sayar da giyar da giya kwalba 177 da burkutu jarka 1 da tukunyar dafa burkuntu.

Kwamandan Hisba na jiha, Mallam Dahiru Garki yace sun gudanar da aikin ne bisa tallafin majalisar sarkin Gumel.

a wani labarin mai alaka da wannan, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gargadi al’ummar Musulmi da su guji kin yin azumin watan Ramadan da gangan.

A wani sakon murya ta WhatsApp da ya aika wa kungiyoyin yada labarai a Kano, kwamandan hukumar Hisbah na jihar, Haroun Ibn-Sina, ya ce hukumar ba za ta kyale duk wanda aka samu yana cin abinci da rana ba tare da wani kwakwakwaran dalili ba.

A cewarsa, hukumar Hisbah ba za ta nade hannunta tana ganin yadda matasa musulmi ke keta hurumin addinin Musulunci a jihar ba, musamman a wannan wata mai alfarma, inda ake bukatar musulmi su gudanar da cikakkiyar ibada ga Allah.

Haruna Ibn-Sina ya kara da cewa, hukumar Hisbah ba za tayi kasa a gwiwa ba, wajen gudanar da aikinta na tabbatar da cikakken bin tsarin shari’ar Musulunci a cikin watan Ramadan da ma bayansa, inda ya ce duk wanda aka samu yana saba wa Shari’a, za a hukunta shi.

Haruna Ibn-Sina ya jaddada cewa Hisbah ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na yaki da badala a Kano.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + twelve =