Buhari ya yafewa tsaffin gwamnoni biyu dake gidajen yari

71

Majalisar magabata ta kasa ta yi afuwa ga tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da Jolly Nyame na jihar Taraba, wadanda ke zaman gidan yari bisa samun su da laifin cin hanci da rashawa.

Gwamnonin na daga cikin fursunoni 159 da majalisar ta yi wa afuwa a zamanta wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ba a samu cikakken jerin sunayen wadanda aka yiwa afuwar ba.

A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, an yi wa tsoffin gwamnonin biyu afuwa ne bisa dalilai na lafiya da kuma shekaru.

Jolly Nyame mai shekaru 66, gwamnan jihar Taraba ne daga shekarar 1999 zuwa 2007, yana zaman gidan yari na tsawon shekaru 12 a gidan yarin Kuje bisa samunsa da laifin karkatar da kudaden jama’a, a lokacin da yake kan mulki.

A daya bangaren, Joshua Dariye mai shekaru 64, wanda ya mulki jihar Filato a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, an daure shi ne bisa laifin satar naira miliyan dubu 2 na dukiyar al’umma a lokacin da yake gwamna.

Sharhi 1

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 + 7 =