Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Abdulganiyu Jaji a matsayin sabon shugaban hukumar kashe gobara ta tarayya daga ranar 22 ga Afrilu.
Hakan yazo a wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakatariyar hukumar kula da hukumomin civil defense, immigration da gidajen yari, Aisha Rufa’i, da ta fitar jiya a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, Abdulganiyu Jaji ya kasance mataimakin Konturola Janar mai kula da harkokin gudanarwa da kayayyaki a hukumar kashe gobara ta tarayya kafin a nada shi a matsayin Konturola Janar.
Ya karbi mukamin ne daga hannun mukaddashin Kwanturola janar, Samson Karebo, wanda ya karbi ragamar shugabancin hukumar bayan da tsohon konturola janar Ibrahim Liman yayi ritaya.
Rahoton ya ce sabon kwanturola janar din ya fara aiki a ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya a shekarar 1991.