Buhari ya gargadi kasashen waje kan tsoma baki a zaben Najeriya

46

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya yi gargadi kan tsoma bakin kasashen waje a zaben 2023 a Najeriya.

Ya yi wannan gargadin ne a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja a yayin wani liyafar buda baki da jami’an diflomasiyya.

Shugaba Buhari ya sha alwashin yin amfani da duk wata halastacciyar hanya don kare kuri’un ‘yan Najeriya a lokacin babban zaben 2023.

Ya ce masu shirin magudin zabe su sake shawara.

Dangane da rikicin Rasha da Ukraine, Shugaba Buhari ya yi kira da a kara kula da yanayin jin kai a yankunan da rikicin ya shafa.

Ya kuma yi gargadin cewa rikicin zai kara ta’azzara idan ba a samu matsaya cikin gaggawa ba.

A wani labarin kuma, babban limamin fadar shugaban kasa, Sheikh Abdulwahid Sulaiman, a jiya ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsaya tsayin daka kan maslahar kasa, ya kuma tabbatar da cewa ba a barnatar da gwagwarmayar da Nijeriya ta yi da sadaukarwar da ta yi a shekara mai zuwa ta zaben da ke tattare da rashin tabbas.

Limamin, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a masallacin fadar shugaban kasa yayin kammala tafsirin da Shugaba Buhari da sauran musulmai suka halarta.

Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari ya samu yabo daga Sheikh Sulaiman bisa sadaukarwar da ya yi da kuma gaskiya da rikon amana da sadaukar da kai ga al’umma.

Ya ce shugaba Buhari ya yaba da darussan da ke da alaka da azumin a daidai lokacin da watan Ramadan ke shirin karewa, tare da kawo karshen yawan ibadar da ake yi a watan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − seven =