Buhari ya bayar da umarnin dakile kungiyoyin asiri

49

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga hukumomin tsaro a jihar Ogun da su kawo karshen kungiyoyin asiri a jihar.

Shugaban kasar ya bayar da umarnin cikin wata sanarwa a jiya bayan ‘yan kungiyar asiri sun kashe sama da mutane 16 cikin kwanaki 10 a jihar.

Fada tsakanin kungiyoyin asirin biyu a jihar ya jawo kisan wani shahararren dan daba mai suna Tommy, tare da wasu mutane 15.

An fara fada tsakanin kungiyoyin asirin biyu a ranar Litinin kuma ya ta’azzara bayan kisan Tommy a makon da ya gabata.

Da kadan-kadan fadan ya shiga sauran yankunan jihar bayan na kashe matasa 8 a karamar hukumar Sagamu da wani guda a karamar hukumar Yewa ta kudu.

Shugaba Buhari wanda ya damu da yawan kashe-kashen, ta bakin kakakinsa Mallam Garba Shehu, ya umarci hukumomin tsaro da su dakile duk wasu ayyuka masu alaka da kungiyoyin asiri.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi ganawar sirri da takwaransa na Chadi, Janar Mahamat Deby a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Mahamat Deby, shugaban sojojin rikon kwaryar kasar ta Chadi, a ziyarci Najeriya a watan Mayun bara.

An rawaito cewa shugabannin biyu zasu tattauna akan yakin da ake yi da tayar da kayar baya da ta’addanci a tafkin Chadi inda suka hada iyaka.

Shugaba Buhari da Janar Mahamat Deby sun bi sahun sauran musulmai wajen yin Sallar Juma’a a masallachin fadar shugaban kasa.

Shugaba Buhari a jiya ya tattauna da takwaransa na Nijar, Mohammed Bazoum, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × five =