Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa sabbin kwalejojin polytechnics a wasu sassan kasarnan.
An sanar da amincewar cikin wata sanarwa da aka fitar yau a Abuja ta hannun daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar tarayya ta Abuja, Ben Goong.
Daraktan yace za a kafa sabbin makarantun a jihoshin Kano, Abia da Delta.
A cewar Ben Goong, sabbin makarantun zasu fara harkokin koyo da koyarwa a watan Oktoban bana.
A wani batun kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kwarin gwiwar cewa bukatar Najeriya na fadada yankin ruwanta, a karkashin dokokin majalisar dinkin duniya na ruwa, yana bisa turba.
Shugaba Buhari ya sanar da haka yau a Abuja lokacin da ya karbi wani rahoto daga kwamitin shugaban kasa akan bukatar fadada yankin ruwan kasarnan.