An yankewa tsohon shugaban Burkina Faso hukuncin daurin rai da rai bisa kisan Thomas Sankara

53

An yankewa tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore hukuncin daurin rai da rai bisa kisan gillar da aka yi wa Thomas Sankara wanda ya gabace shi.

An kashe Thomas Sankara mai shekaru 37 a duniya tare da wasu 12 a lokacin juyin mulkin shekarar 1987 wanda ya kawo Blaise Compaoré kan karagar mulki.

Shugabannin biyu sun kasance abokai na kut-da-kut kuma tare suka kwace mulki a shekarar 1983.

Thomas Sankara ya kasance gwarzo ga mutane da yawa a duk fadin Afirka saboda matsayinsa na adawa da mulkin turawa da salon rayuwa mai sauki.

Bayan ya kwace mulki yana dan shekara 33 kacal, dan juyin juya halin ya yi gangamin yaki da cin hanci da rashawa tare da kara kudaden ilimi da kiwon lafiya.

Mai gabatar da kara ya ce an yaudari Thomas Sankara zuwa wani taro na majalisar juyin juya hali ta kasa inda aka kashe shi.

A cewar kwararrun masana da suka bayar da shaida a lokacin shari’ar, an harbi Thomas Sankara a kirji har sau bakwai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − fourteen =