Shugaban Tunisa ya rushe majalisar kasar

43

Shugaban kasar Tunisiya Kais Saied ya rusa majalisar dokokin kasar da ya dakatar watanni takwas da suka gabata sakamakon zanga-zangar da aka yi a kasar.

Hakan dai ya zo ne yayin da ‘yan majalisar suka gudanar da wani taro ta internet a jiya inda suka kada kuri’ar soke dokar shugaban kasar da ta ba shi kusan dukkan madafun iko tun bara.

Shugaban kasar ya kira matakin na majalisar a matsayin yunkurin juyin mulki.

Ya ce majalisar ta rasa halaccinta sannan ta ci amanar kasa, kuma za a gurfanar da ‘yan majalisar da ke da hannu a gaban kuliya.

Kais Saied ya dakatar da majalisar dokokin kasar, ya karbi dukkan madafun iko sannan ya fara yunkurin sake rubuta kundin tsarin mulkin watanni takwas da suka gabata.

Tun daga wannan lokacin, bacin rai akan yanayin tattalin arziki a Tunisiya ya haifar da zanga-zangar kan tituna, inda wasu masu zanga-zangar suka yi arangama da ‘yan sanda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 + three =