Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna wanda yanzu zai zama mukaddashin gwamnan jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce Gwamna Ganduje ya tafi kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda zai halarci taron zuba jari da kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) za ta shirya.
Ya ce an baiwa mataimakin gwamnan ikon yin cikakken aiki har sai lokacin da Gwamna Ganduje ya dawo.
Sanarwar ta umurci dukkanin kwamishinonin da shugabannin ma’aikatu, manyan jami’an gwamnati, kamfanoni da daidaikun mutane da su baiwa mukaddashin gwamnan goyon baya da hadin kai.
Sannan ya kuma kara da cewa duk al’amuran da ke neman kulawar gwamna a tuntubi ofishin mukaddashin gwamna.