Bankin Duniya ya ce adadin talakawan Najeriya zai kai miliyan 95 da dubu 100 a bana.
Bankin ya bayyana haka ne a rahotonsa na tantance talauci.
Rahoton ya yi nuni da cewa rikicin corona na kara haifar da talauci a Najeriya, inda ya kara tura karin mutane miliyan 5 cikin talauci nan da shekarar 2022.
Kasancewar cigaban tattalin arzikin daidaikun mutane yayi rauni sosai ta kowane bangare a shekarar 2020, bankin ya ce ana hasashen talauci zai kara kamari ga matalauta na yanzu, yayin da wadanda ke kusa da layin talauci kafin rikicin corona za su iya fadawa cikin talauci.
Rahoton ya lura cewa cigaban Najeriya yana raguwa tun kafin rikicin corona.
A bara ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta tsamo ‘yan Najeriya miliyan 10 da rabi daga kangin talauci tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.