Yanzu-yanzu: Atiku ya ziyarci Obasanjo

64

A safiyar yau da misalin ƙarfe goma na safe, Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gidansa dake Abeokuta.

Tin bayan ƙaratowar zaɓukan shekarar 2023 dai ƴan siyasa suna ta neman giyon bayan jiga-jigan ƙasa domin tabbatar da cikar burinsu.

Atiku dai shine mataimakin Obasanjo daga 1999 zuwa 2007, kafin daga bisani alaƙa tai tsami a tsakanin su.

A ziyarar ta Atiku yau Asabar sun shiga ganawar sirri inda daga bisani ake sa ran jin abin da aka tattauna.

Ƙarin bayank na nan tafe…

📸 Facebook/Atiku Abubakar

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 2 =