‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 11 a Neja

60

Gwamnatin jihar Neja ta ce ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 11 da wasu mutanen kauyuka a wasu hare-hare tsakanin ranar Juma’a da Asabar a kananan hukumomin Shiroro da Paikoro na jihar.

Mazauna yankunan sun ce akalla mutane 32 ne aka kashe a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Gwamnan jihar Abubakar Bello yayi magana akan hare-haren a yau ta wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Mary Noel-Berje ta fitar.

Ya ce an kuma kashe da dama daga cikin ‘yan bindigar.

Abubakar Bello ya ce za a iya dakile hare-haren da ake kaiwa Galadiman Kogo da wasu kauyukan karamar hukumar Shiroro idan mutanen yankin suna sanar da jami’an tsaro kan lokaci.

Tun da farko, shugaban karamar hukumar Shiroro Suleiman Chukuba ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin amma ya ce bai iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 + 9 =