Shugaban Ukraine yace an kashe mutane 137 da raunata 316 a mamayar Rasha

170

A cigaba da mamayar kasar Ukraine, sojin Rasha da sanyin safiyar yau sun harba makaman roka kan babban birnin Ukraine Kiev.

Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter.

Ministan ya yi nuni da cewa, Ukraine za ta yi galaba a kan Rasha kamar yadda ta yi nasara a kan Jamus.

Sai dai shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce an dakatar da sojojin Rasha daga matsowa kasar ta bangarori da dama.

A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin, shugaba Zelenskyy ya ce hare-haren na Rasha an kai su ne kan sojoji da fararen hula.

Wani hari da aka kai da makami mai linzami kan iyakar Ukraine da ke yankin kudu maso gabashin kasar, ya yi sanadiyyar mutuwar wasu masu gadi.

Yankin dai ba shi da iyaka da kasar Rasha amma yana bakin tekun Azov da ya raba kasashen.

A halin da ake ciki, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy a cikin wani faifan bidiyo ya ce an kashe fararen hula da sojoji 137 a kasar a ranar farko ta mamayar Rasha tare da jikkata 316.

Ya bayyana wadanda abin ya shafa a matsayin jarumai.

Ya ce sojojin Rasha suna kashe mutane tare da mayar da garuruwan zaman lafiya zuwa sansanin soji, inda ya kara da cewa wannan zalunci ne kuma ba za a yafe ba.

Ana sa ran adadin zai karu bayan hare-haren baya-bayan nan, ciki har da wadanda aka kaddamar a birnin Kyiv da safiyar yau.

Ya kuma bayyana takaicinsa kan sakamakon tattaunawar da ya ce ya yi da shugabannin kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO.

A cewar kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Filippo Grandi, sama da ‘yan Ukraine dubu 100 ne suka kauracewa gidajensu domin neman tsira, sannan dubbai ne suka tsallaka zuwa kasashen Moldova, Romania da sauran kasashe makwabta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × two =