Iyalan Marigayi Habeeb Idris da aka kashe a rikicin hijabi da aka sake samu a makarantar sakandare ta Oyun Baptist dake Ijagbo tare da wasu musulmin jihar Kwara sun bukaci gwamnatin jihar ta biya diyyar naira miliyan 113 da dubu 388.
A baya dai musulmi da iyalan sun mayar da naira miliyan 1 da gwamnatin ta yi wa iyalan mamacin bayan wata ganawa da sakataren gwamnatin Jihar, Farfesa Mamman Jibril.
Musulman 11 da suka samu munanan raunuka a yayin harin sun kuma mayar da kudi dubu 250 da gwamnatin jihar Kwara ta ba su ta cikin wasikar Abdullahi Abubakar da wanda abin ya shafa, Taofeeq Mustafa a madadin kungiyar musulmin Offa da Oyun.
Da yake yiwa manema labarai jawabi yau a Ilorin, babban birnin jihar, shugaban matasan musulman jihar Kwara, Ustaz Abdurrazzaq Al-Amin, ya roki gwamnatin jihar da ta bayar da isassun kudade ga musulmi 11 da suka jikkata a rikicin hijabi na Ijagbo.
A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta dauki nauyin biyan kudaden asibiti da kuma kudaden da aka kashe na wadanda suka jikkata a lokacin rikicin.