Mutanen da suka mutu a guguwar Batsirai a Madagascar sun karu zuwa 30

89

Yawan mutanen da suka mutu a mahaukaciyar guguwar Batsirai wacce ta bar kasar Madagascar a ranar Litinin da safe, sun karu zuwa 30, kamar yadda a adadin da hukumomi suka sabunta, kuma zai iya karuwa kasancewa ana cigaba da samun gawarwaki daga baraguzan gidajen da suka rushe.

Hukumar kula da annoba ta Madagascar a yau da safe ta sanar da cewa yawan wadanda suka mutu a kasar wacce tsibiri a tekun India, sun karu daga 21 zuwa 30.

Hukumar tace mutane dubu 94 ne guguwar Batsirai ta shafa kuma mutane dubu 60 a yanzu basu da muhalli.

Kungiyoyi dayawa masu zaman kansu da hukumomin majalisar dinkin duniya sun fara aikawa da kayayyakin tallafi da ma’aikata domin taimakawa wadanda annobar ta shafa tare da jawo mamakon ruwan sama da guguwa mai gudun kilomita 165 a kowace awa.

Guguwar ta auwaka kasar Madagascar cikin gaggawa lokaci daya daga Asabar da Lahadi.

Kasar ta Madagascar na kokarin farfadowa daga guguwar Ana wacce ta shafi mutane akalla dubu 131 a fadin kasar karshen watan da ya gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 1 =