
Majalisar dattawa a yau ta zartar da kudirin kafa sabbin makarantun horas da lauyoyi a yankuna 6 na kasarnan.
Hakan ya biyo bayan amincewa da wani rahoton kwamitin shair’ah da hakkin bil’adama na majalisar, karkashin shugabancin Sanata Opeyemi Bamidele na jam’iyyar APC daga jihar Ekiti.
Makarantun horas da lauyoyi da ake dasu a halin yanzu akwai a Lagos (Kudu maso Yamma) da Abuja (Arewa ta Tsakiya) da Yola (Arewa maso Gabas) da Kano (Arewa maso Yamma) da Enugu (Kudu maso Gabas) da kuma Yenagoa (Kudu maso Kudu).
Karin makarantun horas da lauyoyi da aka amince da su sun hada da ta Kabba a jihar Kogi (Arewa ta Tsakiya) da ta Maiduguri a jihar Borno (Arewa maso Gabas) da ta Argungu a jihar Kebbi (Arewa maso Yamma) da ta Okija a jihar Anambra (Kudu maso Gabas) da ta Orogun a jihar Delta (Kudu maso Kudu) da ta Ilawe a jihar Ekiti (Kudu maso Yamma) da kuma ta Jos a jihar Filato (Arewa ta Tsakiya).
A wani labarin kuma, majalisar dattawa a yau ta karbi wata wasika daga shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ta nadin Shu’aibu Lau daga jihar Taraba a matsayin sabon mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar.
Iyorchia Ayu yace nadin Shu’aibu Lau yazo ne sanadiyyar sauyin shekara da Emmanuel Bwacha yayi daga jam’iyyar ta PDP zuwa APC a makon da ya gabata.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar a gaban zauren majalisar.
A wani batun kuma, tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Emmaneul Bwacha daga jihar Taraba, ya sanar da sauyin shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Sauyin shekar ta Emmanuel Bwacha ta kara yawan sanatocin jam’iyyar APC zuwa 70, na PDP 38 sai sanata daya daga jam’iyyar YPP.
Ya sanar da matakin nasa na sauyin shekar a gaban zauren majalisar yayi zaman majalisar.