Majalisa ta nemi a dauki mataki akan kashe-kashen matsafa

52

Majalisar Wakilai ta yi kira da a dauki matakan tunkarar matsalolin dake jawowa da kawo karshen yawaitar kashe-kashen matsafa a kasarnan.

Bayan amincewa da kudiri da Toby Okechukwu na jam’iyyar PDP daga jihar Enugu ya gabatar a zauren majalisar a yau, majalisar ta yi nuni da cewa matsalar kashe-kashen matsafa ta yi matukar tayar da hankali a Najeriya a ‘yan kwanakin nan.

Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar ya bayyana cewa ana samun yawaitar kashe-kashen matsafa tare da yawaitar sace-sacen mutane da bacewar mutane a sassa daban-daban na kasarnan.

Ya ce, a mafi yawan lokuta, masu laifin su kan yi fyade, da raunata wadanda zasu kashe, da kisa da kuma cire sassan jikin wadanda ba su ji ba basu gani ba, don yin tsafi.

Don haka majalisar ta yi kira ga Sufeto-Janar na ‘yansandan kasarnan da ya dauki matakin gaggawa na kara sanya ido da tattara bayanan sirri da nufin kamawa tare da hukunta duk masu aikata kisan gilla a Najeriya.

A halin da ake ciki, Majalisar Wakilai ta zartas da wani kudirin doka da zai tanadi tarar Naira miliyan 500 ga jami’an gwamnati da suka saba wa tanadin dokar kiwon lafiya ta kasa ta shekarar 2014 tare da gudanar da tafiye-tafiyen neman lafiya da kudaden jama’a, zuwa karatu na biyu.

Kudirin wanda Sergius Ogun na jam’iyyar PDP daga jihar Edo ya dauki nauyinsa, na neman yin gyara ga dokar lafiya ta kasa ta shekarar 2014.

A muhawarar da ya jagoranta, dan majalisar ya ce dokar da ake da ita ba ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ba, don haka ne ake shirin yi wa dokar kwaskwarima.

Ya ce babban makasudin kudurin shi ne a yi wa babbar dokar kwaskwarima ta yadda za a sanya takunkumi ga duk wani jami’in gwamnati da ya saba wa tanadin dokar, musamman sashe na 46.

Ya kara da cewa gyaran da aka yi shi ne a hana jinya a kasashen waje lamarin dake illata asibitocin cikin kasa.

Dan majalisar ya kara da cewa, kudirin dokar zai karfafa bukatar sake fasalin yanayin kiwon lafiya a kasarnan da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 9 =