Jigawa ta samu N13bn saboda zama ta daya a gaskiya da adalchi

294
Gwamnan Jihar Jigawa Muhammadu Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ayyana cewa jihar ta karbi tallafin kudi naira miliyan dubu 13 saboda kokarinta a shirin tabbatar da gaskiya da adalchi wanda gwamnatin tarayya ta assasa tare da hadin gwiwar Bankin Duniya.

Gwamnan ya sanar da haka lokacin da yake karbar tawagar bincike ta shirin daga ma’aikatar kudi ta tarayya, inda yace jihar ta karbi jumillar kudi naira miliyan dubu 13 kashi biyu, saboda kasancewarta jihar da tazo ta daya a shirin.

Badaru Abubakar yayi bayanin cewa jihar ta ciyo kudi dala miliyan 750 a shekarun 2018 da 2019.

Gwamnan ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da Bankin Duniya bisa shirin tare da yin alkawarin cigaba da tabbatar da dorewar gaskiya da adalchi wajen gudanar da gwamnatinsa.

A jawabinsa tunda farko, jagoran tawagar kuma mataimakin daraktan shirin a ma’aikatar kudi ta tarayya, Alhaji Ali Muhammad, yace sun zo jihar Jigawa ne domin ganawa da masu ruwa da tsaki a shirin da nufin jin ta bakinsu a nasarori da kalubalen da shirin ke fuskantar a jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + 1 =