INEC ta sanar da sabbin ranakun zaben 2023

101

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da sabbin ranakun gudanar da babban zaben shekarar 2023.

A baya hukumar ta sanar da ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 domin zaben shugaban kasa. Sai dai, shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya gayawa manema labarai cewa an fitar da sabbin ranakun gudanar da zaben.

A cewarsa, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihoshi a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2023.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan kudirin dokar zabe a jiya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + five =