Gwamnatin Tarayya za ta kashe N62bn kowace shekara akan masu HIV

20

Gwamnatin Tarayya a kokarinta na kawo karshen barazanar cuta mai karya garkuwar jiki, ta sanar da shirye-shiryenta na kashe kudi naira miliyan dubu 62 kowace shekara domin yiwa masu cutar magani.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne yayi alkawarin a yau lokacin da yake kaddamar da gidauniyar cuta mai karya garkuwar jiki ta naira miliyan dubu 62.

Yayi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da bayar da fifiko a ayyukan da suka shafi harkokin kiwon lafiya domin dakile cutar da sauran cutukan da suke addabar al’umma.

Shugaba Buhari, cikin wata sanarwa da kakakinsa, Femi Adesina, ya fitar yace hadin gwiwar Najeriya da bangaren kungiyoyi masu zaman kansu domin dakile annobar corona ya samar da hanyoyin samun kudaden da za ayi amfani da su domin dorewar kula da cutar ta HIV.

Shugaba Buhari ya yabawa hukumar kula da cuta mai karya garkuwar jiki ta kasa (NACA) da kungiyar dake yaki da cutar a Najeriya bisa kokarinsu na samar da gidauniyar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × three =