Gwamnatin Tarayya ta mika titi mai tsayin 10km ga gwamnatin Jigawa

43
Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar

Ma’aikatar aikin gona tarayya ta mikawa gwamnatin jihar Jigawa aikin titin karkara mai tsawon kilomita 10 domin saukaka jigilar kayan amfanin gona da manoma ke yi a kokarin tallafawa noman abinci.

Da yake jawabi a wajen bikin mika ayyukan ga jama’a, darakta kuma kodinetan ayyuka na ma’aikatar noma ta tarayya reshen jihar Jigawa, Mustapha Ibrahim Anka, ya ce an gudanar da aikin ne da nufin tallafawa manoman karkara domin zuwa kasuwa.

Ya bayyana cewa, an gudanar da aikin ne a wurare daban-daban, wanda ya sa aka hada dubunnan manoma da kasuwa domin samun saukin jigilar kayayyakin amfanin gona.

Ibrahim Anka ya kara da cewa, baya ga ayyukan hanyoyin, ma’aikatar ta kuma aiwatar da ayyukan samar da wutar lantarki masu amfani da hasken rana guda takwas domin samar da ababen more rayuwa da za su inganta rayuwar manoman karkara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − 5 =