Gwamnatin Kano ta maka wanda ya kashe Hanifa a gaban kotu

29

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar Noble Kids, da laifin yin garkuwa da dalibarsa mai shekaru 5, Hanifa Abubakar, tare da abokan ta’asarsa guda biyu Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin a gaban wata babbar kotu a jihar.

Darakta mai shigar da kara ta jihar, Aisha Mahmoud, ta bayyana hakan a yau a lokacin da aka sake gurfanar da mutanen uku a gaban wata kotun majistare dake zamanta a Gidan Murtala.

Ta ce an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban alkalin kotun majistiren mai shari’a Muhammad Jibril, duk da cewa kotun ba ta da hurumin yin shari’ar irin wadannan manyan laifukan, amma don sanar da ita cewa gwamnatin jihar ta shigar da kara a gaban babbar kotun.

Aisha Mahmoud ta kara da cewa an shigar da karar ne a babbar kotu, a gaban mai shari’a Usman Na-Abba, bisa umarnin alkalin alkalan jihar.

A halin da ake ciki kuma, tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muaz Magaji, zai kara kwana daya a gidan yari, bayan dage shari’ar sa zuwa ranar Juma’a.

Muaz Magaji mai sukar gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yana fuskantar tuhume-tuhume guda hudu da suka hada da bata sunan mutum, cin mutunci da gangan, karya da kuma tada zaune tsaye ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin a cigaba da tsare shi a gidan yari tare da dage sauraren karar saboda yanke hukunci kan bukatar belinsa.

A wani labarin kuma, dakataccen shugaban hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin-Gado, ya kalubalanci dakatar da shi a gaban kotun ma’aikata.

Magaji Rimin-Gado ya shigar da karar ne yana kalubalantar dakatarwar inda yake tuhumar gwamnatin jihar Kano da wasu mutane biyar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two − one =