Gwamnati za ta horas da malaman makaranta 45,000

70

Gwamnatin tarayya ta sanar da horon komfuta ga malaman makaranta dubu 45 a fadin jihoshi 24.

Magatakardar hukumar yiwa malaman makaranta rijista, Farfesa Josiah Ajiboye, ya sanar da haka lokacin kashi na uku na shirin horas da malaman makaranta akan ilimin komfuta na GPE.

Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta mika karamin kwamitin kula da shirin horas da malaman makaranta na GPE ga hukumar.

A cewar Ajiboye, an tsara bayar da horon domin magance matsalar da barkewa annobar ya haifar ga tsarin ilimin kasarnan.

Ya sanar da cewa a kashin farko an zabe Jigawa, Benue, Bauchi, Ebonyi, Enugu, Gombe da sauran jihoshi 10 domin bayar da horon.

Ya kara da cewa shirin horaswar zai koyar da malamai da shugabannin makarantu ilimin komfuta domin shiryawa wajen kula da lafiya a makarantu ciki har da cutar corona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 5 =