Gwamnati za ta hada gwiwa da Japan domin samar da lantarki

49

Gwamnatin Tarayya tace tana shirin hada gwiwa da hukumar hadin kan kasa da kasa ta kasar Japan wajen aiwatarwa da fadada ayyukanta na samar da wutar lantarki.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na ma’aikatar wuta ta tarayya, Odutayo Oluseyi, ya fitar a Abuja.

Oluseyi yace ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, ya sanar da haka lokacin da ya karbi tawaga daga hukumar ta kasar Japan a ofishinsa dake Abuja.

Ministan yace manufar hakan shine fadada hanyoyin samar da wutar lantarki domin tallafawa masana’antu a jihoshin Lagos da Ogun.

Ya tabbatarwa da hukumar jajircewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wajen tabbatar da gudanar da aiki mai kyau kamar yadda ya kamata a cigaban gine-ginen samar da wutar lantarki a Najeriya.

Ministan yace samar da wutar lantarkin abu ne mai muhimmanci ga gwamnati wanda aka nufi ingantawa zuwa matakin da ake bukata musamman a yankunan dake samun habakar masana’antu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + 19 =