Gwamnati Tarayya ta amince da dawowar jigilar Emirates

31

Gwamnatin Tarayya ta amince da dawowar kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates a Najeriya.

Gwamnati ta kuma bukaci hukumomi a Hadaddiyar Daular Larabawa da su amince da bukatar kamfanin Air Peace na komawa jigilar fasinja farawa daga ranar 1 ga watan Maris.

Hakan na kunshe ne cikin wata wasika daga hannun Darakta Janar na hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa Kaftin Musa Nuhu wacce aka aikawa darakta janar na hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Hadaddiyar Daular Larabawa, Saif Mohammed Al Suwaid.

Wasikar ta kuma ce gwamnatin tarayya ta amince da matsalar tsaron lafiya, bayan bangarorin da suka kamata sun bibiyi hakan.

Hukumomi a Hadaddiyar Daular Larabawa sun kakabawa Najeriya da sauran kasashen Afirka 11 dokar hana shiga kasar, a wani bangare na matakan dakile bazuwar cutar corona.

Kafin kakabawa dokar wacce ta fara aiki a ranar 25 ga watan Disambar bana, Hadaddiyar Daular Larabawa da Najeriya basu jima da shawo kan wani rikicin diplomasiyya tsakaninsu ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × three =