ECOWAS ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulki a Guinea Bissau

37

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yi Allah wadai da abin da ta kira yunkurin juyin mulki a kasar Guinea-Bissau, tare da yin kira ga sojoji da su koma barikokinsu.

Hakan ya biyo bayan rahoton wasu mutane sanye da kayan fararen hula sun bude wuta kusa da wani ginin gwamnati da ake gudanar da wani taro tsakanin shugaban kasar da firaministan kasar ta Guinea-Bissau, wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.

An rufe makarantu da ofisoshi domin yin taka tsan-tsan, sannan an tura sojoji zuwa wasu gine-ginen gwamnati.

A halin da ake ciki, ministar harkokin wajen Guinea-Bissau Suzi Barboza ta shaidawa manema labarai cewa, a halin yanzu tana kasar waje kuma tana jiran labari dangane da shugaban kasar.

An zabi shugaba Umaro Sissoco Embaló, wanda shi kansa tsohon firaminista ne, a matsayin shugaban kasa a shekarar 2020 bayan da ya lashe zaben fidda gwani da ya yi da wani tsohon firaminista.

Shugaba Embaló ya ce yana son warware rikicin siyasa a kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 + fifteen =