Buhari ya rattaba hannu akan dokar zaben da aka yiwa gyara

70
Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan kudirin dokar zabe da aka yiwa gyara kuma ya zama doka.

Shugaban Kasar ya sanya hannu akan kudirin a fadar shugaban kasa a gaban shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran jami’an gwamnati.

Sanya hannu akan kudirin yazo ne kwanaki kadan bayan kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya tabbatar da cewa shugaba Buhari zai sanya hannu akan kudirin.

Kafin ya sanya hannu akan kudirin, shugaban kasar ya nemi a yiwa kudirin gyara inda ya bukaci majalisun kasa su goge wani sashe na kudirin wanda ya haramtawa masu rike da mukaman siyasa tsayawa takara a zabe.

Shugaban kasar yace sashen ya dakile yancin masu rike da mukaman siyasa na tsayawa takara a zabe da zaben wani dan takara a dukkanin tarukan jam’iyyun siyasar kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × one =