“Ban aikata ba” —Abdulmalik ya musanta garkuwa, kisan Hanifa

142

Mai makarantar Nobles kids Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa da kuma kashe dalibarsa, Hanifa Abubakar, mai shekara 5, ya musanta garkuwa da kuma kashe ta a gaban kotu.

A yau Litinin ne dai a ka sake kawo Tanko, shi da abokan aikata laifin da a ke zargi, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin a gaban Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin Alƙali Usman Na-Abba.

Bayan da a ka karanto musu tuhume -tuhumen da a ke yi musu, dukkan su sun musanta.

Da a ke tuhumar Tanko cewa ya yi garkuwa da kuma kashe Hanifa, sai ya ce “ban aikata ba.”

Ƙarin bayani na nan tafe…

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − four =