An tsige Mahdi, an rantsar da Nasiha a Zamfara

104

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamnan jihar Barista Mahdi Aliyu Gusau.

A yayin zaman da ya gudana a yau, mambobi 20 cikin guda 24 sun kada kuri’ar amincewa tsige mataimakin gwamnan, bayan gabatar da rahoton kwamitin da aka kafa domin bincikensa bisa tuhumar sa da aikata laifuka.

Kakakin majalissar, Honorable Nasiru Mu’azu Magarya shine ya karanta rahoton.

Tunda farko a yau, kwamitin da aka kafa mai wakilai 7 domin binciken zargin yin ba daidai ba da cin amanar aiki akan Mahdi Gusau, ya kammala zamansa tare da mika rahotonsa.

Da suke mika kwafin rahoton ga kakakin majalisar, ‘yan kwamitin sun ce basu da hurumin yin magana da kowa akan rahoton.

A yayin da yake nasa jawabin, kakakin majalissar, yace zasuyi aiki akan rahoton da aka gabatar kamar yanda sashe na 188 na kundin mulkin kasa ya amince.

Ya godewa ‘yan kwamitin bisa gudanar da aikin su, kamar yanda doka ta tanada.

A wani labarin kuma, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya zabi sanata Hassan Muhammad a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.

Wannan na zuwa ne bayan tsige Barista Mahdi Aliyu Gusau.

Gwamna Bello Matawalle ya aika da wasika zuwa ga majalissar dokokin jihar, yana bukatar da a tantance Hassan Nasiha.

Kakakin majalissar Honarable Nasiru Mu’azu Magarya shine ya karanta wasikar gwamnan yayin zaman majalissar na yau.

Sabon mataimakin gwamnan Hassan Nasiha an fara zabar sa a matayin sanata a shekarar 2007, kuma a yanzu shine dan majalissar dake wakilta Zamfara ta tsakiya a majalissar dattawa ta kasa.

Ya rasa kujerar sa a shekarar 2011, inda ya sake dawowa a shekarar 2019 bayan kotun koli ta soke zaben ‘yan jam’iyyar APC a jihar.

Sai dai, lokaicin da Bello Matawalle ya koma jam’iyyar PDP a shekarar 2021, Hassan Nasiha ya bi shi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 + 3 =