An kama mutane 400 bisa zanga-zangar adawa da yaki a Rasha

149

Kimanin mutane 400 ne aka kame jiya a yayin sabuwar zanga-zangar adawa da mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine, a cewar masu rajin kare hakkin jama’a.

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta tabbatar da gudanar da zanga-zangar a biranen Rasha 17.

Hotuna da bidiyo akasari daga birnin St Petersburg da aka watsa ta dandalin sada zumunta na Telegram sun nuna jami’an ‘yan sanda suna amfani da karfin tuwo wajen murkushe zanga-zangar.

Yawancin Rashawa suna da kusanci da ‘yan Ukraine, galibi saboda alakar jini kuma sun fito don nuna juyayi.

Zanga-zangar ta jiya bata kai ta farko ba da aka yi a ranar Alhamis, inda aka kama sama da mutane dubu 1 da 700 a fiye da birane 40.

A baya dai hukumomin Rasha sun fitar da gargadin gaggawa game da zanga-zangar tare da yin barazanar kame.

Hukumomin kasar sun sha haramta yin zanga-zangar, tare da fakewa da annobar corona.

A wani labarin kuma, ministan lafiya na kasar Ukraine Viktor Liashko a yau ya ce fararen hula 198 ne aka kashe kawo yanzu a yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.

Ministan ya ce akwai yara uku daga cikin wadanda suka mutu.

Ya ce mutane dubu 1 da 115 sun samu raunuka, ciki har da yara 33.

Tun farko dai rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ya ta’azzara ne lokacin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da fara wani farmaki na musamman na soji a ranar Alhamis.

Dakarun Rasha sun tunkari babban birnin Ukraine a yau bayan da aka kwashe dare ana tashin bama-bamai da fadan akan tituna, inda suka kori mazauna Kiev babban birnin kasar, wadanda suka gudu neman mafaka a dakunan karkashin kasa, wasu kuma sun bazu a kan iyakokin kasar domin gujewa yakin.

Duk da cewa Rasha ta yi ikirarin cewa hare-haren da take kaiwa kan Ukraine tana nufar sojoji ne kawai, lamarin ya rutsa da fararen hula.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 − 9 =