‘Yan jam’iyyar PDP 4,000 sun koma APC a Jigawa

39

Jam’iyyar APC a jihar Jigawa tace ta kammala shirye-shiryen karbar ‘yan jam’iyyar PDP su dubu 4.

Shugaban jam’iyyar APC na jiha, Aminu Sani Gumel, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na kasa a jiya cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata domin karbarsu.

Sani Gumel yace tun a baya karin wasu ‘yan jam’iyyar PDP sama da dubu 2 sun yi watsi da jam’iyyarsu zuwa APC a kananan hukumomin Kafin Hausa da Maigatari.

Yace ‘yan jam’iyyar PDP dubu 4 sun nuna sha’awar kaura zuwa APC a kananan hukumomin Garki da Birnin Kudu, inda ya kara da cewa nan gaba kadan za a gudanar da bikin karbarsu.

Sani Gumel ya danganta nasarorin da jam’iyyar APC ta samu da shugabanci nagari na shugaban kasa Muhammadu Buhari a matakin tarayya tare da na gwamna Muhammad Badaru Abubakar a matakin jiha.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × two =