Tarayyar Turai za ta kakabawa Mali takunkumi

29

Kungiyar Tarayyar Turai tace za ta kakaba takunkumi akan kasar Mali bayan shugabannin kasar na soja wadanda suka yi juyin mulkin bara, sun karya alkawarinsu na gudanar da zabe a watan gobe.

Hakan ya biyo bayan makamancin matakin daga kungiyar cigaban tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS) wacce a ranar Lahadi ta sanar da takunkumin kasuwanci tare da rufe iyakoki.

Da yake sanar da matakin kakaba takunkumin, shugaban huldar kasashen waje na Tarayyar Turai, Jospeh Borrel, yace duk da gargadin da aka sha yiwa hukumomin Mali, har yanzu babu wata alamar cigaba.

Yace an kuma kababa takunkumin a matsayin martanin zuwan sojojin kwangila na kasar Rasha.

Kasashen Afrika ta yamma da Tarayyar Turai na fatan matakan zasu matsawa shugabannin sojoji suyi watsi da shirye-shiryensu na mulkar kasar na karin wasu shekaru, su kuma gudanar da zabuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − 2 =