NNPC na bukatar N3trn domin biyan kudin tallafin mai a bana

18

Kamfanin mai na kasa NNPC ya bukaci jumillar naira tiriliyan 3 daga gwamnatin tarayya domin samar da kudaden tallafin mai a shekarar da muke ciki.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ta sanar da haka a jiya lokacin da take jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan zaman ganawar majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar a Abuja.

Zainab Ahmed tace ana bukatar kimanin naira tiriliyan uku domin cigaba da biyan tallafin man fetur.

Ministar tace majalisar ta amince da ra’ayin gwamnonin jihoshi da suka ce akwai bukatar a rage yawan adadin kudaden.

Zaman ganawar na majalisar zartarwa ta tarayya ya kuma amince da bukatar gyara dokar kasafin kudin bana wanda za a aikawa majalisun kasa.

A zaman ganawar majalisar wanda aka gudanar a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari jiya a Abuja, an kuma amince da kudi naira miliyan dubu 52 da miliyan 800 domin kammala ayyukan wasu tituna guda 3 a fadin kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 5 =