Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, yace majalisar dattawa za ta yi aiki tare da hukumomin tara kudaden shiga wajen rage yawan basukan da kasarnan ke ciyowa.
Sanata Ahmad Lawan ya sanar da haka jiya a Abuja, a wajen wani bikin cikarsa shekara 63 a duniya.
Yace majalisar dattawa zata tallafa da sanya ido akan hukumomin wajen tabbatar da suna yin abin da ya kamata.
Ahmad Lawan ya kara da cewa majalisar dattawa a bana za kuma ta mayar da hankali akan tsaro ta sanya ido sosai akan kudaden da aka warewa sojoji da hukumomin tsaro a kasafin kudi.
Yayi bayanin cewa yin hakan zai tabbatar da gaskiya da adalchi wajen sayo kayayyakin aiki da makamai tare da tabbatar da jin dadi da walwalar sojoji da jami’an tsaro wadanda ke da alhakin dawo da tsaro a fadin kasarnan.