Hisbah ta sasanta ma’aurata 3,579 a Jigawa

10

Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta sasanta ma’aurata dubu 3 da 579 a shekarar da ta gabata.

Kwamandan hukumar, Mallam Ibrahim Dahiru, ya sanar da haka a yau yayin wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa a birnin Dutse.

Mallam Ibrahim Dahiru ya bayyana cewa sasanta ma’aurata domin tabbatar da zaman aure cikin lumana na daya daga cikin manyan ayyukan hukumar.

Yace hukumar ta kuma taimaka wajen sasanta rikici tsakanin ‘yan kasuwa 41, iyaye 221 da ‘ya’yansu, makota 319 da kuma manoma da makiyaya 71.

Yace babban aikin hukumar Hisbah shine tabbatar da cewa mutane, ba tare da la’akari da jinsi, shekaru ko sana’a ba, na zama lafiya cikin kwanciyar hankali da lumana.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven − 6 =