Buhari ya soke ziyara zuwa Zamfara

23

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya soke ziyararsa zuwa jihar Zamfara a yau sakamakon rashin kyawun yanayi da ya jawo hazo.

Gwamnan Jihar, Bello Matawalle, ya sanar da haka a yau inda yace shugaban kasar, wanda aka tsara zai taso daga Sokoto a jirgi mai saukar ungulu, dole ya dage ziyarar tasa saboda hazo.

Hukumar kula da yanayi ta kasa tunda farko ta yi hasashen cewa za a samu hazo sosai a jihoshin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, lamarin da ka iya jawowa a soke zirga-zirgar jiragen sama.

A Sokoto, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfanin sarrafa siminti na kamfanin BUA a jihar.

Shugaban Kasar ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, da gwamnan babban bankin kasa (CBN) Godwin Emefiele da shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabi’u da shugaban kamfanin Max Air, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × one =