Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa za a kammala manyan tituna biyu da ake ginawa kafin karshen shekararnan.
Titunan sune babban titin Sagamu zuwa Benin da babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan.
Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, yace shugaba Buhari ya bayar da tabbacin a yau lokacin da yake jawabi ga mazauna jihar Ogun bayan ya kaddamar da wasu manyan ayyuka guda 5 a jihar.
Shugaba Buhari ya yabawa Gwamna Dapo Abiodun bisa gudanar da ayyukan masu ma’ana da hangen nesa domin jama’a, duk da kasancewar ana tsaka da fuskantar alubalen annobar corona.
Shugaban Kasar yayi nuni da cewa manyan ayyukan baza su samu ba, ba tare da sadaukarwar gwamnatin jihar da jajircewarta wajen tsaron rayuka da dukiyar jama’a.
Shugaban kasar ya kuma taya mutanen jihar ta Ogun murnar samun adalar gwamnati mai hangen nesa karkashin jagorancin Dapo Abiodun.