Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Doyin Salami a matsayin babban mai bashi shawara kan tattalin arziki bayan kusan shekara 7 akan mulki.
Wata sanarwa daga mai bawa shugaban kasa shawara kan kafafen yada labarai da huldar jama’a, Femi Adesina, tace Doyin Salami har zuwa yanzu shine shugaban kwamitin bawa shugaban kasa shawara akan tattalin arziki.
A cewar hadimin shugaban kasar, ana sa ran babban mai bawa shugaban kasar shawara kan tattalin arziki zai magance dukkan matsalolin tattalin arziki na cikin kasa, tare da bawa shugaban kasa shawara.
Dr Salami zai kuma sanya ido sosai akan cigaban da ake samu kan tattalin arziki a cikin kasa da kasashen duniya, tare da tsara wasu tsare-tsare da bawa shugaban kasa shawara akan dokokin tattalin arziki domin daidaita tattalin arziki da habaka cigaba da samar da ayyukan yi da kakkabe fatara da talauci, da sauransu.
Doyin Salami babban malamine a makarantar kasuwanci ta Lagos inda yake jagorantar azuzuwan yanayin tattalin arziki da kasuwanci.