An kashe fararen hula 108 a hare-haren sama a Habasha

8

Majalisar dinkin duniya (MDD) tace akalla fararen hula 108 aka kashe a hare-haren jiragen sama a arewacin kasar Habasha cikin makonni 2 da suka gabata.

Ofishin kula da hakkin bil’adama na majalisar dinkin duniya yace an raunata wasu mutane 75 a hare-haren, wadanda ake zargin dakarun sojin saman Habasha ne suka kaddamar.

Gwamnatin tarayyar Habasha tun a baya ta musanta kai hari akan fararen hular yankin Tigray.

Fadar gwamnatin dake Addis Ababa, babban birnin kasar, a jiya ta bukaci shugaban hukumar lafiya ta duniya (WHO), Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, da ya dena magana akan halin da ake ciki a yankin Tigray.

Dr. Tedros, wanda ya fito daga yankin, yace an toshe hanyoyin aikawa da magunguna zuwa ga mutanen yankin.

A wani lamarin mai alaka, shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya yayi gargadin cewa ayyukansa a arewancin Habasha sun kusa tsayawa cak sanadiyyar kazamin fadan da ya jawo toshe hanyoyin shigar da mai da kayan abinci.

Babu wata motar kayan agaji da ta samu isa yankin Tigray cikin wata guda, kuma shirin abinci na majalisar dinkin duniya yace kayayyakin sun kusa karewa.

Akwai karancin kayan aiki da magunguna a cibiyoyin lafiya da asibitoci bayan an hana shigowa da kayayyakin kiwon lafiya tsawon watanni.

Kamar yadda yazo a kididdigar majalisar dinkin duniya, sama da kashi 90 cikin 100 na mutanen yankin na tsananin bukatar agajin gaggawa.

Hanya daya tilo ta zuwa yankin Tigray ta ratsa ne ta yankin Afar dake makotaka.

Tafiyar da kayan tallafi akan hanyar na yawan fuskantar cikas daga fada da jinkirin shirye-shirye.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five − two =