Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu masu garkuwa da mutane 14 da suka kashe jami’an ‘yan sanda biyu kwanan nan tare da yin garkuwa da wani dan kasuwa a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Aliyu Sale Tafida ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a yau a hedikwatar ‘yan sandan da ke Dutse, babban birnin jihar.
An rawaito cewa wasu ‘yan bindiga sun yi wa tawagar ‘yan sandan kwanton bauna, inda suka kashe jami’ansu biyu tare da kona motar da suke sintiri a garin Kwalam da ke karamar hukumar Taura a jihar.
Kwamishinan ya ce kama wadanda ake zargin ya biyo bayan wani samame da rundunar ta gudanar na yaki da duk wani nau’in miyagun laifuka a jihar.
Aliyu Tafida ya ce an kama wadanda ake zargin yayin da aka kai farmaki kan maboyar batagari guda uku a kauyukan Dajin Maizuwo, Dan Gwanki da Yandamo duk a karamar hukumar Sule-Tankarkar ta jihar.
Tafida ya ce a yayin farmakin an kama mutane 10 maza da mata 4 wadanda ake zargin 2 daga cikinsu sun jikkata sakamakon musayar wuta da suka yi tare da jami’an ‘yan sanda.